1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Kudu za ta samar da riga-kafi

July 21, 2021

Kamfanin samar da riga-kafi a kasar Afirka ta Kudu Biovac, ya ce zai fara samar da riga-kafin annobar corona ta kamfanin BioNTech/Pfizer a kasar.

https://p.dw.com/p/3xoKk
Corona Impfstoff Moderna Biontech Pfizer
Hoto: Marcus Brandt/dpa/picture alliance

Hakan na zuwa ne biyo bayan cece-kucen da ake yi kan rashin adalci wajen samar da riga-kafin annobar, inda kasashe matalauta da masu tasowa suka dogara kan kasashe masu karfin tattalin arziki wajen yi wa al'ummarsu riga-kafin.

Karkashin yarjejeniyar da aka samar kamfanin da ke birnin Cape Town, zai kammala matakin karshe ne na riga-kafin tare da rarrabawa a cikin nahiyar bayan samun kayayyakin hadin daga Turai. Ana sa ran cewa kamfanin na Biovac ya samar da allurar riga-kafin corona guda miliyan 100 a duk shekara tare da daukar alhakin rarrabawa kasashe 54 na nahiyar Afirka, ko da yake ana ganin matakin ka iya daukar lokaci.

Tuni dai aka fara samar da riga-kafin kamfanin Johnson & Johnson a kasar. Afirka ta Kudu dai na sa ran yi wa kaso 67 cikin 100 na al'ummarta riga-kafin annobar kafin watan Fabarairun badi, sai dai shirin na samun tsaiko a cewar cibiyar dakile yaduwar cututtuka.