1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Riek Machar ya isa kasar Habasha

Ramatu Garba Baba
June 20, 2018

Tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu, Riek Machar ya isa kasar Habasha don ganawa da shugaba Salva Kiir da zummar samar da mafita daga rikicin yaki na kusan shekaru biyar.

https://p.dw.com/p/2ztAU
Südsudan Präsident Salva Kiir und Vizepräsident Riek Machar
Shugaban Sudan ta kudu Salva Kiir da Riek Machar Hoto: picture-alliance/dpa/P. Dhil

Zaman karkashin jagorancin Firaiministan kasar ta Habasha Abiy Ahmed, zai mayar da hankali kan samar da mafita a rikicin da ya daidaita kasar ya kuma hana ruwa gudu. Wannan shine karon farko da mutanen biyu dake takun saka zasu zauna tare bayan sabanin da ya biyo bayan rushewar yarjejeniyar zaman lafiyan da aka kulla a shekarar 2016 da ya kuma tilastawa Machar din tserewa daga kasar zuwa Afirka ta Kudu don samun mafaka.

Rikicin Sudan ta Kudun, ya janyo asarar rayukan dubban mutane baya ga wasu sama da miliyan guda da suka rasa matsuguninsu suke kuma kasance da rayuwa cikin bukatar taimako.Amman ana fatan ganin zaman na wannan Laraba ka iya yin tasiri a kokarin da ake na ganin bayan yakin.