1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Habasha: Rikicin Tigray ya ci kujerar hafsan sojoji

November 9, 2020

Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya sanar da yin sauye-sauye a shugabancin rundunar sojin kasar da kuma bangaren tattara bayanan sirri.

https://p.dw.com/p/3l2Nb
Abiy Ahmed Äthiopien
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Matakin na Abiy Ahmed din na zuwa ne a ranar Lahadi bayan rahotannin da ke nuna cewa sojojin gwamnati masu yawa sun samu munanan raunuka a rikicin da aka kwashe kwanaki biyar ana tabkawa a yankin Tigray na kasar.


A yanzu Firaministan ya nada Janar Birhanu Jula a matsayin shugaban rundunar sojin kasar, bayan da rahotani ke cewa gwamnati ta sauke tsohon shugaban rundunar daga mukaminsa. A halin da ake ciki kuma sabon shugaban rundunar sojin Janar Birhanu ya sanar da cewa tuni dakarun gwamnati suka tarwatsa wani gungun 'yan tawaye sun kuma lalata makamansu, yana mai cewa sojoji na kara dosawa mafakar 'yan tawayen.

To sai dai Firaminista Abiy Ahmed ya yi kira da a dauki matakan ganin ba a cutar da sauran mazauna yankin Tigray din da ba su ji-ba ba su-gani ba.