Kwace iko daga hannun 'yan tawayen Tigray
November 30, 2020Firamnista Abiy Ahmed na Habasha ya jinjina wa dakarun kasar cikin fafatawa da 'yan tawayen Tigray inda ya ce duk matakan kare fararen hula dakarun sun dauka kuma tuni sun samu galaba kan mayakan 'yan awaren na kungiyar TPLF. A karshen mako gwamnatin Habasha ta aiyana kwace iko da babban birnin yankin Mekelle bayan da sojojin gwamnatin suka kaddamar da farkoki. Firaminista Abiy ya tabbatar wa 'yan kasarsa cewa sojoji ba za su lalata birnin ba.
Zadig Abraha minista mai kula da harkokin dimukaradiyya ya ce dole ne gwamnati ta hana 'yan jarida da sauran jami'ai shiga yankin sakamakon yanayin da ake ciki. "Ba mu ne ke toshe komai ba yanayin da ake ciki ne, akwai aiyuka na soja wannan ka iya zama hadari ga rayuwa, a lokaci guda 'yan ware sun kaste layukan waya, sun lalata hanyoyin da filayen jiragen sama. Muna aiki sake ginawa. Idan babu wadanann abubuwa ba wanda zai iya shiga samun wani bayani, ba abin da muke boyewa." Daruruwan mutane sun halaka yayin da dubban suka tsere daga gidajensu sakamakon rikicin na kusan wata guda.
Karin Bayani: Murkushe 'yan aware da karfin tuwo a Habasha
Jagoran 'yan waren Debretsion Gebremichael na yankin na Tigray ya nemi gwamnatin Habasha ta dakatar da abin da take yi na rashin tunani kuma suna nan kusa da babban birnin yankin Mekelle inda suke ci gaba da fada. Ya fadi haka yayin hira da kamfanin dillancin labaran AP sannan Gebremichael mai shekaru 57 da haihuwa ya musanta rahoton ya tsere gudun hijira zuwa Sudan ta Kudu.
Karin Bayani: Kyautar Nobel ga Abiy Ahmed
'Yan waren sun fusata da matakin Firaminista Abiy Ahmed na rage tasirin yankin ta mayar da yawan dakaru zuwa kashi daya cikin hudu, maimakon kashi 60 cikin 100 da suke da shi gabanin ya dauki madafun iko, kana suna ganin gwamnatin kasar duk matakan da take dauka na tsangwama musu ne. Ita dai Tigray People's Liberation Front (TPLF) a baya ke rike da madafun ikon Habasha kimanin shekaru 30 har zuwa shekara ta 2018.