1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO ta nuna damuwa kan yankin Tigray

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 12, 2021

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya nuna damuwarsa kan yadda rayuwar al'ummar yankin Tigray na Habasha ke cikin hadari.

https://p.dw.com/p/42waE
Äthiopien I Krise in Tigray
Al'ummar Tigray cikin mawuyacin haliHoto: Ben Curtis/AP/picture alliance

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniyar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya nuna damuwar tasa ne tare da yin gargadin cewa al'ummar yankin na cikin halin matsananciyar yunwa da ka iya halaka su, baya ga wadanda ke mutuwa sakamakon rashin magunguna. Ghebreyesus da shi ma ya fito daga yankin arewacin Tigray din, ya yi wannan gargdin ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishin hukumar ta WHO da ke Geneva. A cewarsa hukumar ba za ta iya tura kayan agaji zuwa yankin na Tigray ba, sakamakon yadda aka killace yankin baki daya. Firaminista Abiy Ahmed na Habasha, ya kwashe tsawon shekara guda yana fafata yaki da mayakan yankin na Tigray, wadanda a yanzu haka suke kokarin isa Adis Ababa babban birnin kasar.