Gyaran kundin tsarin mulki a Moritaniya
August 7, 2017Talla
Shirin yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulki wanda shugaban kasar ta Moritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz ke son yi ya tanadi soke majalisar dattijai tare da maye gurbinta da ta wakillan yankuna da kuma sauya fasalin tutar kasar ta hanyar kara wasu jajayen launuka biyu a samanta da nufin karrama kushewar abin da gwamnatin ta kira shahidai na kasa wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen kalubalantar mulkin mallakar da Faransa ta yi wa kasar wanda kawo karshe a shekara ta 1960. Sai dai tuni kawancan jam'iyyun adawar kasar wanda da ma ya yi kira ga magoya bayansa da su kauracewa zaben ya yi watsi da sakamakon nasa.