1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gyaran fuska ga tsarin shige da fice a Faransa

Ahmed Salisu
December 19, 2023

Jam'iyyar National Rally da ke kyamar baki a Faransa ta bayyana cewar za ta goyi bayan jam'iyyar Shugaba Emmanuel Macron wajen amincewa da kudurin doka da zai yi gyaran fuska ga tsarin shige da fice na kasar ta Faransa.

https://p.dw.com/p/4aMRx
Debatte vor der Präsidentschaftswahl in Frankreich
Hoto: Ludovic MARIN/AFP

Shugabar jami'iyyar ta National Rally, Marien Le Pen, ta ce muhimmancin kudurin dokar ne ya sanya ta ga dacewar yin aiki da Macron a wannan gabar, sai dai Macron din da jam'iyyarsa na shan suka daga 'yan jam'iyyarsa da ke da ra'ayin mazan jiya.

Nan gaba a yau ne dai za a kada kuri'a domin amince da kudurin dokar ko kuma yin watsi da shi a majalisar dokokin kasar.