1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus na fuskantar barazanar sake yaduwar cutar corona

Ramatu Garba Baba
October 9, 2020

Gwamnatin Jamus ta ce tana shirin daukar karin sabbin matakai don ganin ta hana yaduwar cutar corona, a daidai lokacin da alkaluma na masu kamuwa da cutar mai kama numfashi ke haurawa.

https://p.dw.com/p/3jhHo
USA Coronavirus Impfstoff-Test (picture-alliance/AP Photo/H. Pennink)
Hoto: H. Pennink/AP Photo/picture-alliance

Gwamnatin Jamus ta ce tana shirin daukar karin sabbin matakai don hana yaduwar cutar corona. Karfafa matakan zai zama dole ne, muddun aka ci gaba da samun karuwar alkaluma na wadanda cutar ke kamawa nan da kwanaki goma masu zuwa.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da magadan garin wasu jihohin kasar, sun amince da a bai wa jihohin kasar damar tuntubar cibiyar  Robert Koch da ke sanya idanu kan cututtuka masu saurin yaduwa, don neman taimako na yakar annobar da kawo yanzu ke ci gaba da yaduwa a sassan duniya.

Alkaluman yawan masu kamuwa da cutar corona a kasashen duniya, ya saka gwamnatoci maido da matakan kulle da hana taron jama'a. Indiya na daga cikin kasashen da yawan masu cutar suka zarta miliyan shida, a Faransa ma gwamnati ta kara matakan hana yaduwar cutar. A kasar Guatemala, fadar shugaban kasar ta ce manyan jami'an gwamnati kimanin 58 ne suka kamu da corona.

Baki daya corona ta halaka mutum sama da miliyan daya bayan bullarta a Disambar bara a yayin da ta kama wasu sama da miliyan talatin.