1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gwamnatin sojin Nijar ta soke yarjejeniyar soja da Amurka

March 17, 2024

Gwamnatin sojin jamhuriyar Nijar ta soke yarjejeniyar soja ta hadin gwiwa da kasar Amurka wace aka rattaba a shekarar 2012 da nufin yakar kungiyoyin jihadi a yankin Sahel.

https://p.dw.com/p/4doUM
Gwamnatin sojin Nijar na shirin korar sojoji Amurka
Gwamnatin sojin Nijar na shirin korar sojoji AmurkaHoto: Télé Sahel/AFP

Sanarwar katse huldar sojan tsakanin Nijar da Amurka na zuwa ne sa'o'i kadan bayan da wata tawagar Amurkawa da ta ziyarci Nijar ta gaza yin tozali da shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Janar Abdourahamane Tiani.

A cikin wata sanarwa da kakakin majalisar ceton kasar ta Nijar (CNSP) ya karanta a gidan talabijin mallakar gwamnati, Amadou Abdramane ya bayyana cewa sojojin na Amurka na jibge ne a Nijar ba bisa ka'ida ba, kana kuma hakan ya saba wa ka'idoji da dokokin kundin tsarin mulkin kasar da ke yankin Sahel.

Kazalika ya kuma yi Allah wadai da zargin nuna isa da shugabar tawagar Amurkawan Mme Phee ta nuna a lokacin ziyarar kwanaki uku da suka kai Nijar a farkon wannan mako, abin da ya kira da yunkurin lalata huldar da ke tsakanin kasashen biyu.

Kimanin sojojin Amurka 1,100 ne ke girke a Nijar domin yakar kungiyoyin jihadi baya ga kuma wani babban sansani na jirage marasa matuka a jihar Agadez da ke arewacin kasar.

Karin bayani:  Amurka za ta mayar da sojojinta Agadez 

Bayan korar sojojin Faransa, wannan yunkuri na raba gari da Amurka na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin na Nijar ke karfafa hulda da wasu kasashe inda Rasha da Iran ke a sahun gaba.