1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Siriya ta sallami firsinoni 550

November 6, 2011

A yunƙurin neman sulhu da masu zanga-zanga, gwamnatin Siriya ta yi belin wasu daga dubban firsinonin da ta cafke

https://p.dw.com/p/135u8
Hoto: dapd

Gwamnatin ƙasar Siriya ta yi belin firisonin fiye da 500 daga cikin mutanen da ta cafke a wuraren zanga-zangar neman sauyi.

Shugaba Basahar Al Assad ya ce ya ɗauki wannan mataki domin mutunta yarjejeniyar da ya cimma tare da Ƙungiyar ƙasashen larabawa, wadda ta tanadi belin dukan firsinoin siyasa.

Saidai duk da sallamar mutanen fiye da 500, Ƙungiyar ƙasashen labarawa ta bayyana rashin gamsuwa game da yadda jami´an tsaron ƙasar Siriya ke ci gabada hallaka masu zanga-zangar.

A wata arangama da aka gwabza jiya a birnin Homs mutane 13 sun rasa rayuka.

Daga ɓarkewar rikicin Siriya zuwa yanzu, alƙallmu sun ce fiye da mutane 3000 suka rasa rayuka.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmad Tijani Lawal