1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin rikon kwarya ta kasar Somaliya zata koma Mogadishu daga 21 ga wata

February 9, 2005

Gwamnatin hijira ta kasar Somaliya dake Kenya ta ce zata fara hada-hadar mayar da mazauninta zuwa Mogadishu tun daga 21 ga wannan wata

https://p.dw.com/p/BvdH
Sabon shugaban Somaliya Abdullahi Yusuf Ahmed
Sabon shugaban Somaliya Abdullahi Yusuf AhmedHoto: AP

Tuni dai gwamnatin ta tura wata tawagar bin bahasi zuwa Mogadishu misalin makonni biyu da suka wuce domin gane wa idanuwanta halin da ake ciki. Piraminista Muhammed Ali Gedi ya fada cewar gwamnatinsa zata tashi daga Kenya domin kowa Mogadishu ne sannu a hankali tun daga 21 ga watan fabarairu da muke ciki yanzu. Tawagar bin bahasin ce ta ba da shawarar haka, bayan da ta gane wa idanuwanta halin da ake ciki. Amma kuma piraministan ya kara da cewar hamzarta komawar gwamnatin zuwa Mogadishu ya danganta ne da irin taimakon da zata samu daga waje. Kawo yanzu ba wani cikakken bayanin da aka samu ko dukkan wakilan majalisar ministoci su 42 da kuma na majalisar wakilai su 275 ne zasu koma Mogadishu, abin da ya hada har da shugaba Abdullahi Yusuf. Shi dai piraminista Muhammed Ali Gedi ya ce gwamnatinsa ta gabatar da bayanan shirinta na canza mazauni da kuma kasafin kudinta da ya tanadi dala miliyan 77 dangane da watanni shida masu zuwa ga cibiyoyin ba da lamuni na kasa da kasa. Ya ce wannan gwamnati ‚yar jaririya ce kuma tana bukatar taimako na kasa da kasa kafin ta samu ikon tsayawa kan kafafuwanta. Wadannan kudade za a yi amfani da su ne domin hada-hadar canza mazaunin gwamnatin da kirkiro mahukuntan tsaro da kwance damarar dakarun sa kai da sauran ayyukan gudanarwa. To sai dai kuma duka-duka taimakon da gwamnatin ta samu bai zarce na dala miliyan shida ba. Sanarwar canza mazaunin dai ta zo ne jim kadan bayan da haulakan yakin Somaliya suka mika fadar mulki da gidan rediyo kasa da kuma babbar tashar jiragen ruwa zuwa ga hannun gwamnatin ta wucin gadi. Ita ma kungiyar tarayyar Afurka AU, a ranar litinin da ta wuce, ta tsayar da shawarar tura sojojin kiyaye zaman lafiya, wadanda zasu sa ido akan matakan komawar gwamnatin zuwa fadar mulki ta Mogadishu. Babban aikin dake gaban gwamnatin shi ne sake maido da oda a kasar Somaliya, wadda al’amuranta ya tabarbare baki daya sakamakon shekaru 14 da ta shafe ba tare da wata tsayayyar gwamnati ba. Gwamnatin ta nemi taimakon sojoji dubu 7 da 500 daga kungiyar tarayyar Afurka da ta hadin kan Larabawa, amma kawo yanzu ba a tsayar da shawara akan yawan sojojin da za a tura domin kiyaye zaman lafiyar ba dangane da sabanin dake akwai tsakanin sarakan yakin kasar, inda a waje guda akwai masu adawa da batun sannan a daya wajen kuma akwai masu marhabin da shi bisa sharadin cewar sojojin zasu fito ne daga kasashen da ba su da hannu a rikicin Somaliya.