1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Najeriya ta nada sabon Sefeto janar na yan sandan kasar.

January 25, 2012

Shugaban Najeriya Goodluck Jonatahan ya sallami babban Sifeto janar na kasar Alhaji Hafiz Ringim, inda aka maye gurbinsa da Alhaji Muhammed D. Abubakar. Canjin ya zo lokacin da a birnin Kano ake fama da rashin tsaro

https://p.dw.com/p/13pmo
Nigeria's new acting president and commander in chief Goodluck Jonathan (R) takes his seat at the state house in Abuja, Nigeria 10 February 2010. Nigeria's new acting president and commander in chief Goodluck Jonathan took office in Abuja, Nigeria on 10 February 2010. Nigeria's Senate and House of Representatives on 09 February 2010 both passed motions empowering Vice President Goodluck Jonathan to act as president in the absence of ailing leader Umaru Yar'Adua. Yar'Adua, 58, has been in a Saudi hospital since November 2009 receiving treatment for a heart condition. EPA/STR +++(c) dpa - Bildfunk+++ pixel
Nigeria Goodluck JonathanHoto: picture-alliance/dpa

Alummar anguwar Sheka dake yankin karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano sun fara dawowa cikin hayyacinsu, tun bayan harin da wasu mutane dauke da bindigogi suka kai wa caji ofis din yan sanda a yankin, wadanda ake zaton yayan kungiyar Boko Haram ne suka kai wannan mummunan hari.

Inda suka ringa harbi cikin iska daga bisani kuma suka cinnawa wani sashi na caji ofis din wuta tare kuma da babbake motar yan sandan da ke akan titi.

ausgebrannte Polizeiwache in Maiduguri / Nigeria Ute Schaeffer, 15.06.2011, Maiduguri / Nigeria
Wani ofishin yan sanda da aka kwanaHoto: DW

Abubakar Haruna mazaunin wannan unguwa ne, kuma yace akan idanunsa wannan al'amari ya faru ya bayyana yadda wadannan mutane suka kawo farmakin. Shima wani mutum dake makobtaka da wannan wuri ya bayyana yadda suka kwana cikin firgici a sakamkon karar bindigogi da suka jiyo.

Tun adaren Talata dai sojoji suka mamaye wannan unguwa, amma kafin wayewar gari aka janyesu, lamarin da yasa mutane suka mayar da wurin da abin ya faru wurin kallo.

In this Wednesday, Sept. 28, 2011 photo, police officers armed with AK-47 rifles stand guard at sandbagged bunkers along a major road in Maiduguri, Nigeria. The radical sect Boko Haram, which in August 2011 bombed the United Nations headquarters in Nigeria, is the gravest security threat to Africa's most populous nation and is gaining prominence. A security agency crackdown, which human rights activists say has left innocent civilians dead, could be winning the insurgency even more supporters. (Foto:Sunday Alamba/AP/dapd)
Jami'an yan sandan NajeriyaHoto: dapd

Anata bangaren rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar wannan hari, ta kuma kara da cewa harin ya yi sanadiyyar jikkata jami'an ta guda uku, tare da bayyana cewa za a ci gaba da bincike.

Har ila yau kuma a yammacin Talata ne masu ruwa da tsaki a jihar ta Kano, suka gabatar da wani taro a fadar gwamnatin jihar domin kamo bakin wannan matsaloli. Taron ya sami halartar Mai martaba sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da gwamnan jihar Alhaji Rabi'u Musa Kwankwaso da wasu tsoffin mataimakan gwamnan jihar da malamai da attajirai da sauran al'umma.

Mawallafi: Nasiru Salisu Zango

Edita:      Usman Shehu Usman