Gwamnatin mulkin sojin Mali ta kori Firanministan kasar
November 21, 2024A cikin sanarwar gwamnatin mulkin sojin da aka karanta a kafar talabijin na kasar, ta ce an soke dukannin ayyukan Firanministan da kuma gwamnatinsa. Wannan matakin na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da Firanministan ya caccaki gwamnatin Kanar Assimi Goita, kan rashin cika alkawarin da ta dauka na mayar da kasar kan tafarkin dimokraidyya bayan da ta kwace mulkin kasar da tsinin bindiga.
Karin bayani: Firaiminstan Mali ya kawar da batun shirya zabe nan kusa
Kasar Mali dai ta fuskanci juye-juyen mulki a shekarar 2020 da kuma 2021 sakamakon matsalar tsaron da kasar ta fada. Sojojin dai sun yi alkawarin gudanar da zabe a watan Maris din shekarar 2024 sai dai kuma daga baya sun sanar da dage zaben har sai baba ta gani, inda Janar Goita ya ke ci gaba da kasance shugaban gwamnatin riko.