1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnati Turkiyya ta kori ma'aikata 18.632

Salissou Boukari
July 8, 2018

Gwamnatin Turkiyya ta sanar da korar ma'aikata sama da dubu 18 daga bakin aiki. Tuni dai kudirin ya zama doka ta dindindin da aka wallafa a jaridar kasar ta Turkiyya.

https://p.dw.com/p/312BQ
Symbolbild Polizisten Offiziere Türkei
Hoto: picture-alliance/AA

Daga cikin wadanda aka kora da yawansu ya kai 18.632, akwai 'yan sanda sama da 9000, da sojoji sama da 6000. Sai kuma a fuskar ma'aikatar shari'a akwai mutun kimanin 1000, sannan a ma'aikatar ilimi mutun 650 da dukanninsu aka tabbatar da korarsu daga bakin aiki.

Wannan mataki na karshe na a matsayin hukuncin da ya biyo bayan juyin mulkin da bai yi nasara ba na watan Yulin shekara ta 2016 da aka yi yunkurin yi wa shugaba Erdogan.

A gobe Litinin ne dai Erdogan zai yi rantsuwar kama aiki na sabon wa'adin mulki, inda ake sa ran zai dage dokar ta bacin da kasar ke fuskanta tun bayan yunkurin juyin mulkin. Sannan kuma daga goben ne Shugaba Erdogan ke soma mulki a matsayin shugaban kasa mai cikaken iko bayan sauye-sauye da aka aiwatar a kundin tsarin mulki.