1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

190412 Indien Raketentest

Sonila SandApril 19, 2012

Makamin mai cin dogon zango na Indiya zai iya kai wa Beijing da ke zama babban birnin ƙasar China. Ita ce ƙasa mai tasowa ta farko da ta yi gwajin makami mai linzami.

https://p.dw.com/p/14gzT
An Indian Army multi-barrel rocket launcher fires at 'enemy positions' at an exercise code named "Brazen Chariots" at the Pokharan firing range, in western Rajasthan, India, Wednesday, March 19, 2008. Foreign military observers from 60 countries witnessed the joint army and air force exercise in the desert in the western Indian state of Rajasthan. (ddp images/AP Photo/Mustafa Quraishi)
Agny na biyar shi na makamaki mafi inganci na IndiyaHoto: AP

Ita dai ƙasar ta Indiya ta jinkirta gwajin makamakin nata mai linzama da ta ƙera sakamakon rashin kyau yanayi. Amma kuma daga bisani ta cilla shi daga tsibirinta na wheller i zuwa tekun Indiya ba tare da wata tartibiyar matsala ba, kamar yadda Avinash Chander, shugaban cibiyar ASC da ta ƙera makamin da ke ɗauke a kan nukiliya ya bayyana.

"Wannan gwajin an yi shi cikin nasara. Mun gudanar da shi wannan na farko salin alin kamar yadda muka tanada."

Gwamnatin ta Indiya da ma al'umarta na alfahari da wannan ci gaban da ta samu, a ƙoƙarin da ta ke yi na kama kafar China a fannin makamaki mai linzami. Wannan ƙasa ta Asiya ta daɗe ta na ƙoƙarin shiga cikin ruƙunin ƙasashen duniya da suka ƙera makamin main inganci, wanda kuma zai iya cin dogon zango. A baya dai ta ƙera wasu guda biyu waɗanda nisansu ba zai fi na kilometa 3500 ba. Amma kuma makamain da ta yi gwajinsa a wannan alhamis, wanda ta laƙaba wa suna Agni na biyar, zai iya cin nisan kilometa 5000: ma'ana zai iya kai wa biranen shanghai da kuma Beijing na ƙasar China daga ƙasar ta Indiya. Ko shui ma Baghla Pallav, ƙwararre a fannin tsaron na Indiya, sai da ya zayyana yadda gwajin ya gudana dalla-dalla.

** FILE **In this Jan. 26, 2007 file photo, Indian Army's Brahmos Missiles, a supersonic cruise missile, are displayed during the Republic Day Parade in New Delhi, India. India on Tuesday tested its nuclear-capable Brahmos supersonic cruise missile, jointly developed with Russia, amid mounting tensions with rival Pakistan following the Mumbai terror attacks, a news report said.(AP Photo/Gurinder Osan, File)
Indiya ta dade ta na gwajin makamaiHoto: dapd

" Ko shakka babu,  gwajin dai ya yi nasara. Wannan abin alfahari ne ga ƙasar Indiya da kuma masana kimiyarta. Da ƙarfe 08:07 aka cilla Agni na biyar daga tsibirin Wheller. minti 20 bayan haka kuma makamin ya faɗa cikin tekun Indiya."

Indiya ta tauna aya domin China ta ji tsoro

Tun dai bayan da Indiya ta fara tafiya kafaɗa da kafaɗa da obokiyar gabarta ta fil azam wato pakistan a fannin mallakar makamin ƙare dangi, aka san cewar babu makawa za ta nemi ƙera makamin da China ke alfahari da shi. Duk da cewa ƙasashen biyu wato Indiya da China na kishi tsakaninsu a fannoni da dama ciki kuwa har da na tsaro, amma kuma danganta ta inganta tsakaninsu a fannin tattalin arziki. sai dai har yanzu akwai tsumammiya tsakaninsu game da wani rikici na kan iyaka. Amma a haƙikanin gaskiya, yawan kuɗin da China ta ke kashe wajen saya da kuma ƙera makamai, sun ninka na takwarata ta Indiya. A cewar Raja Mohan, wani masanin siyasar Indiya, ƙasar na da niyar inganta makamin da ta ƙera domin ya yi daidai da na manyan ƙasashen duniya.

"Wannan baje kolin fasaha da muka gani yau, ya na nufin cewar Indiya za ta ci gaba da bunƙasa fusahar ta ta ƙera makamai masu cin dogon zango. Wannan tauna tsakuwa ne domin aya ta ji tsoro. A baya dai, Indiya ba ta da makamin da za ta iya afka wa China da shi."

An Agni IV missile capable of carrying nuclear warhead and a range of 2,500-3,500 kilometers is displayed during the main Republic Day parade in New Delhi, India, Thursday, Jan. 26, 2012. India is marking its 62nd Republic Day with military parades across the country. (Foto:Saurabh Das/AP/dapd)
Indiya na neman kama ƙafar china a yawan makamaiHoto: AP

Ya zuwa yanzu dai, ƙasashe biyar da ke da kujerar dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ne suka mallakai makaman ƙare dangi da kwe cin dogon zango, ciki kuwa har da Amirka, da Faransa, da Birtaniya, da china, da Rasha. Ana jin cewar Indiya na bukatar shekaru kafin makamin da ta yi gwaji ya kama kafafun na waɗanda ƙasashe biyar.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu