1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Koriya ta Arewa ta gargadi ta Kudu

April 3, 2022

Wata shakikiyar Shugaban Koriya ta Kudun Kim Jong Un ta ce ya kamata ministan tsaron Koriya ta Kudu ya shiga 'taitayinsa', domin kalamansa za su janyo wa kasarsa barazana.

https://p.dw.com/p/49ONW
Nordkorea testet Interkontinentalrakete
Hoto: KCNA/KNS/AP/picture alliance

'Yar uwar shugaban kasar Koriya ta Arewa  Kim Jong Un ta siffanta ministan tsaron Koriya ta Kudu da mutum mai ''kalamai marasa ma'ana''. 


Kim Yo Jong na mayar da martani ne a wannan Lahadi biyo bayan kalaman ministan Koriya ta Kudun Kim Suh Wook,  a game da yawaitar gwajin makamai masu linzami da gwamnatin Koriya ta Arewa ke yi a wannan shekara. 

 

Masana dai na siffanta wannan kalaman da cewa akwai yiwuwar Koriya ta Arewa wadda kasashen duniya ke nuna fargabar a kan makamanta na nukiliya, ta ci gaba da yin gwajin makamai masu linzamin da kusan kowane lokaci ke razana makwabciyarta, Koriya ta Kudu.