080611 Jemen Machtkampf
June 8, 2011Wani kakakin gwamnatin Amirka ya ce kashi 40 cikin 100 na gangar jikin shugaba Saleh, ya ƙone. Kuma yanzu haka likitoci a Saudiya, inda ake yi masa jinya, sun fid da wasu ɓuraɓurasan harsasai daga ƙirjinsa.
Da yamma kenan a birnin Sana'a. Da kamata yayi a ce komai na tafiya daidai a babban birnin na Yemen amma sai haushin karnuka da ƙarar harbe harbe ake ji nan da can.
Da safiya ta yi an gano gawawwakin wasu maza su 10 yashe a bakin titi a unguwar Hassaba. Ba wanda ya san wanda ya harbe su har lahira, shin sojojin gwamnati ne suka kashe mayaƙan ƙabilar Ahmar masu adawa a unguwar ta Hassaba. Ko kuma mayaƙan Ahmar ɗin ne suka halaka magoya bayan gwamnati? A halin yanzu dai ba mahalukin da ya san irin abubuwan dake faruwa a Sana'a ba.
Shugaba Abdullah Saleh na samun sauƙi
Janar Yahya Saleh ɗan'uwan shugaba Abdullah Saleh ne. Shi dai janar ɗin shi ne kwamandan dakarun tsaron ƙasa waɗanda aka girke a wasu manyan barikokin soji.
"Shugaban na murmujewa a wani asibitin ƙasar Saudiyya daga raunin da 'yan ta'adda suka yi masa. Nan da makonni biyu zai dawo birnin Sana'a. Kasar sa ta haihuwa tana jiransa, kuma zai ci-gaba da shugabancin ƙasar."
A kan wani tebur dake a ofishin janar Saleh akwai wani mutum mutumin soja riƙe da bindiga da aka rubuta kalmar fatan alheri akai. Wannan dai wata kyauta ce daga Amirka, inji janar ɗin. Amirkawan ne dai suka bawa dakarun tsaron Yemen horon yaƙi da 'yan ta'adda da kuma 'yan tawaye.
"Yanzu ya zama dole mu bincika ko 'yan ƙabilar Ahmar ne ke da alhakin harin na ta'addancin. Za a gudanar da bincike tare da taimakon jami'an shari'a domin gurfanar da waɗanda suka aikata laifin gaban kuliya."
Da wuya a iya tantance sahihancin shari'a a Yemen, ƙasar da a wasu lokutan mutanen da aka harbe su har lahira ke yashe akan tituna.
Ƙarancin ababan more rayuwa a birnin Sana'a
Yanzu haka dai hankalin mazauna birnin Sana'a ya fi karkata ne kan halin rashin sanin tabbas da suke ciki. Harkar samar da wutar lantarki ta gurgunce, ga ƙarancin ruwan sha, gas da kuma man fetir.
A ko-ina aka zaga a birnin dogayen layukan motoci ake gani a gidajen mai, komai ya cakuɗe, kowa tasa ta ishe shi. Ko shin wa ke da laifin wannan mawuyacin hali da al'umar ƙasar ke ciki? Ga dai abin da wani da ya ce ya kwashe kwanaki biyu yana jiran tsammani warabbuka a gidan mai ya ke cewa:
"Saleh ke da laifi. Muna buƙatar sabon shugaban ƙasa wanda zai yiwa ƙasa baki ɗaya aiki amma ba iyalinsa kaɗai ba."
Wasu mazauna Sana'a suna kwanta birnin yanzu da wata jahannama a doron ƙasa.
Mawallafa: Martin Durm / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas