1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwagwarmayar kwato 'yanci a Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou MA
March 29, 2018

A Jamhuriyar Nijar kungiyoyin fararen hular kasar sun ce babu gudu ba kuma ja da baya game da gwagwarmayar da suka runguma duk da kakkame shuwagabanninsu da gwamnati ta yi.

https://p.dw.com/p/2vCp5
Mali Schlange vor Bank
Hoto: Reuters

Hadin gwiwar kungiyoyin sun bukaci jama’a da su shiga wani yajin aikin game gari a ranar biyu ga watan gobe na Afrilu tare da zanga zanga a ranar 8 ga watan. Wannan dai wani sabon salo na takaddamar da kungiyoyin fararen hular suke yi da gwamnati. A wannan Alhamis wasu mambobin kungiyoyin farar hular suka yi ta tofin Allah tsine da matakin da hukumomin kasar suka dauka na rarraba daukacin jiga-jigan kungiyoyin farar hular da ke gwagwarmaya da sabuwar dokar haraji ta wannan shekarar.

Cike makil da ‘yan farar hula da sauran kwarorin ‘yan siyasa na jam’iyyun adawa. Magoya bayan jiga jigan kungiyoyin ne ke nazarin yanda tafiyar ke neman sauyawa da ma irin sabbin matakan da suka cancanci a dauka don cigaba da kokawar. Ko da yake sauran mambobin kungiyoyin na cike da takaicin kakkame shuwagabanninsu, a cewar daukacin mambobin kungiyoyin yanzun ne ma sabuwar tafiya ta soma.

Niger Protest gegen das Haushaltsgesetz der Regierung
Hoto: picture-alliance/AA/B. Boureima

Akalla mutum 22 ne hukumomin kasar suka cafke ciki har da wasu hudu da ke zaman jiga-jigan kungyoyin na farar hula da suka kira zanga-zangar da kuma gwamnatin ta kai ga rarraba su a gidajen yari daban-daban, akalla ko wanne mai nisan fiye tazarar kilomita 100 daga birnin Yamai.

Sai dai duk da yake a yayin sanarwar kungiyoyin sun ce Nouhou Arzika da Moussa Tchangari da Ali Idrissa na cikin koshin lafiya, to amma bai hana matasan ‘yan gwagwarmayar ba nuna wata fargaba.

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin dan adam na cikin gida da na ketare irinsu Amnesty International da Tournon la Page, suka nuna tsananin damuwa tare da kira ga hukumomin Nijar da su saki ‘yan fafutikar inda suka bukaci bangarorin biyu da su saka doka a gaba.