1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adaw su kai kokensu kotu amma ba titi ba

Zainab Mohammed Abubakar
August 7, 2018

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya fadawa shugaba Emmerson Mnangagwa na Zimbabuwe ta wayar tarho cewar, wajibi ne ya dauki mataki kan jami'an tsaronsa bayan kashe mutane shida

https://p.dw.com/p/32m9r
Schweiz - UN-Generalsekretär in Genf
Hoto: picture-alliance/Keystone/C. Zingaro

A wata hirar makamancin wannan, Antonio Guterres ya yi kira ga jagoran adawa Nelson Chamisa da ya kai kokensa gaban kuliya, amma ba kan titi ba, idan har yana kalubalantar nasarar Mnangagwa.

A cewar kakakinsa Farhan Haq, a dukkan wayoyin biyu babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada bukatar jami'an tsaro su yi taka tsan tsan a duk lokacin da suke neman shawo kan wani rikici.