1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Illar sauyin yanayi na karuwa a duniya

Zainab Mohammed Abubakar
August 9, 2021

Bayan da MDD ta gabatar da rahoto mafi tsauri kan illar sauyin yanayi, Chaina na fuskantar karin matsin lamba, kasancewar ita ce kasar da ta fi kowacce fitar da yawan hayaki mai guba.

https://p.dw.com/p/3ykvy
Bangladesch Klimaflüchtlinge Slum Dhaka
Hoto: Getty Images/AFP/M. uz Zaman

Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewar, kasarsa za ta cikanta muradunta na rage hayaki mai gubar da masana'antunta ke fitarwa nan da shekara ta 2030, kana a shekara ta 2060 ta tsabtace kanta daga hayakin baki daya. Sai dai har yanzu babu tsarin da ke kasa, na tabbatar da cimma wadannan manufofi na Chainar.

A daya hannun kuma ministan raya kasashe masu tasowa na Jamus Gerd Mueller, ya ce duniya na bukatar gagarumin mataki na shawo kan matsalar sauyin yanayi, inda ya yi kira ga kasashe matalauta da su kara daukar matakai na kafa dokokin kare yanayi.

A cewar minista Mueller dai, daga cikin kasasahe 191 na duniya, 8 ne kacal ke bin ka'idojin yarjejeniyar da aka cimma a Paris kan rage yawan hayaki mai guba da masana'antu ke fitarwa.