1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jagoran adawa a Guinea ya ce ya lashe zabe

October 20, 2020

Jagoran adawar kasar Guinea Conakry, Cellou Dalein Diallo ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a karshen mako da gagrumin rinjaye.

https://p.dw.com/p/3kBoq
Screenshot auf Zoom | PK Oppositionsführer Cellou Dalein Diallo aus Guinea
Madugun adawar kasar Guinea Cellou Dalein DialloHoto: Cellou Dalein Diallo/Zoom

Babban jagoran adawar Cellou Dalein Diallo kana shugaban jam'iyyar ta Union des Forces Démocratiques ko Democratic alliances, ya bayyana cewa idan aka yi la'akari da kuri'un da aka tattaro daga runfunan zaben kasar, shi ne yayi gagarumar nasara tun a zagayen farko: "Idan aka yi la'akari da adadin kuri'un da aka kada da daukacin sakamakonsu, ni ne na samu rinjaye a zaben tun a zagayen farko."

Karin Bayani: Shugaban Guinea zai nemi wa'adi na uku

Magoya bayan jam'iyyar sun fantsama cikin gari domin soma gudanar da zagayen taya murnarsu jim kadan bayan jawabin jagoran adawar, lamarin da wasu rahotanni suka ce har an samu hargitsi tsakanin magoya bayan jam'iyyar da jami'an tsaro. 
Sai dai jam'iyyar RPG da ke mulkin kasar, ta yi kakkausar suka ga matakin Diallo tana mai cewa ya sabawa ka'ida. Kamar yadda Kiridi Bangoura babban sakataren fadar shugaban kasar kana kakakin jam'iyya mai mulkin ke  cewa: "Wannan dabi'ar ba za ta haifarwa Guinea abin kirki ba, kuma hakan ya yi barra'a da zama cikakken dan jamhuriya. Ina kira ga 'yan kasa na gari da su yi fatali da wannan yunkurin kuma ina fatan hukumomin da suka dace za su dauki matakan da suka cancanta domin hana kasar da hukumomin da ke karkashinta fadawa cikin wani mawuyacin halin na rashin tabbas."

Guinea Präsident Alpha Conde
Dan takarar jam'iyyar RPG mai mulki a Guinea, Alpha CondeHoto: Getty Images/AFP/C. Binani

Karin Bayani:  Guinea Conakry: Kira ga Shugaba Condé

A nata bangaren, hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta bayyana cewa azarbabin da Cellou Dalein Diallo yayi na bayyana kansa a matsayin wanda ya samu nasara, ya taka dokokin kundin tsarin zaben kasar. Tuni dai aka fara samun fashe-fashen wasu wuraren ciki har da wani ofishi, bayan sun kori ma'aikatan da ke ciki. To amma tuni masu fada a ji cikin al'umma ke ci gaba da kiran a sakawa zukata ruwan sanyi, a daidai lokacin da rudani da fargabar tashe-tashen hankula ke ci gaba da kankama.