1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwa ta janyo asarar rayuka a kudancin Afirka

Abdourahamane Hassane
March 19, 2019

Masu aikin agaji a kudancin Afirka na can na kokarin ceto wasu duban jama'ar da suka makale a kan bishiyoyi da runfin gidaje a kudancin Afirka.

https://p.dw.com/p/3FJYu
Simbabwe Zyklon Idai Zerstörte Brücke
Hoto: picture-alliance/AP Photo/T. Mukwazhi

Bayan ficewar guguwar da ake yi wa la'akabi da sunan Idai wada ke tafe da iska mai karfin gaske hade da ruwan sama wace ta ratsa kasashen kudanci na Afirka. Masu aiko da rahotannin sun ce ruwan sama da ake ci gaba da shatatawa kamar da bakin kwarya na yin baranaza ga rushewar wasu madatsun ruwa a yanki. Guguwar wace ta share garuruwa da dama a Mozambik da kuma gabashin Zimbabuwe kawo yanzu ta kashe mutane 182.