1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwar Eunice ta kada a Turai

Abdourahamane Hassane MAB
February 20, 2022

Guguwar Zeynep ko Eunice wacce ta kada a yanki Arewa maso yammacin nahiyar Turai, ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla guda 16 tare da haddasa mummunar asara ta kadarori.

https://p.dw.com/p/47IpW
BDTD Sturm Eunice - Großbritannien
Hoto: Jacob King/AP/dpa/picture alliance

Guguwar wacce ke hade da ruwa da iska mai karfin gaske da ta taso daga Ireland ta ratsa kasashen Birtaniya da Faransa kafin ta zarce zuwa kasashen Denmark da Jamus. A Jamus sama da kilomita 100 na hanyoyin  layin dogo sun lalace, sakamakon faduwar bishiyoyi, abin da ya gurgunta al'amuran sufuri a yankin arewacin kasar.

A yankin arewaci na Turai kuwa, an soke tashi da sauka na jiragen sama saboda iska mai karfi da ta barke. Mutane akalla biyu suka mutu a Jamus, hudu a Holland, uku a a Ingila, biyu a Beljiyam, daya a Ireland, kana wasu shida a Poland yayin da gidaje dubu 130 suka rasa wutar lantarki.