1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Guguwar ''Ciaran'' ta halaka mutane a yammacin Turai

November 3, 2023

Wata mummunar guguwa mai suna "Ciaran" da ke gudun kilomita 200 a cikin sa'a guda ta ratsa wasu sassan Yammacin nahiyar Turai tare da haddasa ruwan sama mai yawa.

https://p.dw.com/p/4YLs2
Guguwar ''Ciaran'' ta halaka mutane a yammacin Turai
Guguwar ''Ciaran'' ta halaka mutane a yammacin TuraiHoto: Stephane Mahe/REUTERS

Akalla mutane bakwai hukumomi suka tabbatar da mutuwarsu yayin da dama suka jikkata a Kudu maso yammacin Ingila da Arewa maso yammacin Faransa da iftila'in ya shafa.

Karin bayani: Mutane fiye da 20 suka halaka sakamakon guguwa mai karfi a turai

Sannan sama da gidaje miliyan guda sun rasa wutar lantarki a kasar Faransa, yayin da bishiyoyin da suka fadi suka toshe hanyoyin motoci da layin dogo. A gundumar Finistère ta kasar Faransa ga misali, an yi asarar dukiya mai yawa bayan ratsawar guguwar mai tsayin fiye da mita 20 a tsakiyar yammacin nahiyar Turai.

Karin bayani: Guguwa ta dakatar da jiragen sama a Jamus