1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane shidda sun rasa rayukansu a Girka

Zulaiha Abubakar
July 11, 2019

Akalla mutane shidda sun rasa rayukansu yayin da gommai suke kwance cikin mawuyacin hali a asibiti sakamakon iska mai karfi da tsawa a arewacin kasar Girka

https://p.dw.com/p/3Lt3V
Nordgriechenland Griechenland Unwetter
Hoto: Reuters/A. Konstantinidis

Gabanin faruwar wannan ibtila'i dai wata iska mai karfi ce ta fara kadawa a arewa maso gabashin yankin Halkidiki wacce ta haifar da rushewar manyan gine-gine da fizgo bishiyoyi tun daga tushe da kuma kifar da ababen hawa, a nata bangaren hukumar kula da yanayi a kasar ta Girka ta bayyana cewar wannan shine karon farko da kasar ta fuskanci irin wannan iska mai karfin gaske a tarihi duk kuwa da yanayin zafi da ake ciki. Daga cikin wadanda suka rasa rayyukansu har da 'yan yawon bude ido daga kasashen Rasha da Romaniya.