1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gudunmawar Amirka ga yaƙi da ta'addanci

June 4, 2013

Al'ummar Najeriya na mayar da martani kan kyautar zunzuruntun kuɗin da Amirka ta alƙawarta, ga duk wanda ya ba da bayyanan da za su kai ga zaƙulo jagorar ƙungiyar Boko Haram da wasu ƙungiyoyin da ke yammacin Afirka

https://p.dw.com/p/18jfn
This image taken from video posted by Boko Haram sympathizers shows the leader of the radical Islamist sect Imam Abubakar Shekau made available Wednesday Jan. 10, 2012. The video of Imam Abubakar Shekau cements his leadership in the sect known as Boko Haram. Analysts and diplomats say the sect has fractured over time, with a splinter group responsible for the majority of the assassinations and bombings carried out in its name. (AP Photo) THE ASSOCIATED PRESS CANNOT INDEPENDENTLY VERIFY THE CONTENT, DATE, LOCATION OR AUTHENTICITY OF THIS MATERIAL
Hoto: AP

Yayin da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana goyon baya ga matakin gwamnatin Amurka na sa kuɗi dalar Amirka miliyan bakwai ga wanda ya taimaka aka kai ga kame jagoran ƙungiyar Boko Haram, masharhanta da talakawa na bayyana cewa matakin ba zai taimakawa ƙoƙarin kashe wutar rikicin ba.

Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ta bakin kakakin sa Rueben Abati ya goyi bayan matakin gwamnatin ƙasar Amurka na sanya zunzurutun kudi dalar Amirka miliyan Bakwai ga duk wanda ya bada bayanai da suka kai ga kame jagoran Kungiyar gwagwarmayan nan da aka fi sani da Boko Haram.

Shugaban ya haƙiƙance cewa matakin zai taimaka gaya wajen yaƙin da yanzu haka Tarayyar Najeriyar ke yi da ƙungiyar Jama'atu Ahlul Sunnan Lidda'awati Wal Jihad wanda aka fi sani da Boko Haram.

epa03046191 (FILE) A file photograph Goodluck Ebele Jonathan, President and Commander-in-Chief of the Armed Forces of the Federal Republic of Nigeria speaks during the general debate at the 66th session of the United Nations General Assembly at United Nations headquarters in New York, New York, USA, on 21 September 2011. Media reports state on 31 December 2011 that President Goodluck Jonathan has declared a state of emergency in areas affected by attacks from the Islamist group Boko Haram. Borders will be temporarily closed in the north-eastern states of Yobe and Borno, and central state of Plateau. EPA/JASON SZENES *** Local Caption *** 00000402928322 +++(c) dpa - Bildfunk+++
Shugaba Barack Obama na AmirkaHoto: Reuters

Yaya yankin Arewacin Najeriya ke kallon wannan mataki?

Sai dai wannan mataki bai samu goyon bayan yawancin al'ummar ƙasar ba musamman waɗanda ke yankin Arewacin kasar da suke ganin matakin a matsayin ingiza mai kantu ruwa da ƙasar ta Amurka ke yiwa Najeriya.

Yawancin al'umma kasar sun yi imanin cewa matakin na ƙasar Amurka zai ƙara hura wutar wannan rikici ne maimakon kawo karshen sa bisa la'akari da irin wannan matakan da kasar ta ɗauka a baya wanda kuma ba su taimakawa yaƙin da ake da ‘yan ta'addar ba.

Da dama na ɗaukar goyon bayan da gwanmatin Najeriya ta baiwa matakin ƙasar Amirkan a matsayin kasawa tare da yin sakaci a ƙoƙarin magance matsalar cikin gidan kasar. Malam Umar Adamu Shine shugaban ƙungiyar Malamin jami'an jihar Gombe.

Ra'ayin talakwan Najeriya dangane da wannan batu

Ga talakawan ƙasa kamar Malam Muhammad Mai kayan miyan Orji Quarters na ganin wannan matakin ba zai haifar da komai ba sai ƙara rura wutar rikicin.

A baya ma dai gwamnatin ƙasar Amurka ta sanya maƙudan kuɗaɗe kan wasu da take nema ruwa jallo sai dai hakar ba ta kai ga cimma ruwa ba. Wannan ya sa na tambaya malam Ibrahim Gombe kan irin tasirin ko akasin haka da wannan mataki zai yi a kokarin da ake da kawo karshen yaƙin da ake yi da Kungiyar Ahlul Sunna da aka fi sani da Boko Haram sai ya kada baki ya ce.

Na Kuma tambaya Malam Muhammad Bello Sarkin Arewan Bolari malami a sashin tarihi na jami'ar jihar Gombe ko kwalliya ta taba biyan kudin sabulu dangane da irin wannan mataki ? Sai ya ce.

U.S. President Barack Obama speaks about his administration's counterterrorism policy at the National Defense University at Ft. McNair in Washington, May 23, 2013. Obama outlined plans on Thursday to limit the use of U.S. drone strikes and took steps aimed at breaking a deadlock on closing the military prison at Guantanamo Bay, Cuba. REUTERS/Larry Downing (UNITED STATES - Tags: POLITICS MILITARY)
Shugab Goodluck Jonathan na NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa

A baya ma dai Tarayyar Najeriya ta ware kuɗi naira miliyan hamsin ga wanda ya bada bayanan da suka taimaka wajen kame Imam Abubakar shekau amma har yanzu shiru ka ke ji kamar an shuka dusa.

Mawallafi: Amin Mohammed Suleiman
Edita: Pinaɗo Abdu Waba