1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Goodluck Jonathan ya kori shugaban hukumar NNPC

June 29, 2012

Sabon yanayi na kwararar 'yan ci rani yan Afirka zuwa kudancin nahiyar na haddasa damuwa.

https://p.dw.com/p/15O46
Hoto: picture-alliance/dpa

To madallah. Jaridun na Jamus a wannan ako sun duba al'amura da dama da suka shafi nahiyar Afirka, tun daga matakin da shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya dauka na koran shugaban kamfanin man fetur na kasar, wato NNPC, har ya zuwa ga matsalar yan ci-rani na kasashen Afirka dake kwarara zuwa kudancin nahiyar da halin da ake ciki a Sudan.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a wannan mako ta duba batun cin hanci ne da yayi kanta a Najeriya. A daidai lokacin da hukumar man fetur ta kasar take cikin wani hali na fadi-tashi da kuma binciken kwamitin majalisar dokoki tattare da abin kunyar tallafin farashin man fetur, shugaban kasa, Goodluck Jonathan yace ya lashi takobin kawo karshen cin rashawa a hukumar, inda matakin farko shine na koran shugaban ta da wasu manyan ma'aikata. Jaridar tace wannan mataki ne da tuni ya kamata a dauke shi, saboda binciken kwamitin majalisar dokoki da aka gabatar a watan Aprilu ya nuna cewar tsakanin shekara ta 2009 zuwa 2011, kwatankwacin Euro miliyan dubu biyar da dari biyar ne ya bace daga wannan hukuma. A madadin Austen Oniwon da aka kora, Jonathan yanzu dai ya nada Andrew Yakubu, wanda dama ya dade a hukumar ta NNPC a matsayin sabon shgaban ta.

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung a wannan karo ta duba wani sabon yanayi ne a nahiyar Afirka, inda yan ci rani suke kara kwarara yankin kudancin Afirka. Jaridar tace Afirka ta kudu tana neman zama dandalin tara yan ci rani, musamman daga Habasha da Somalia ko Eritrea. Sai dai kuma mafi yawan yan ci ranin, ana masu romon baka ne kawai , saboda sai sun biya kudi mai yawa kafin yan baranda ko yan fasa-kwari su kwashe su su zuwa Afirka ta kudun, inda daga karshe sukan zama basu da aikin yi, babu wurin zama, babu abinci ba kuma wata makoma garesu. Hukumar dake kula da kaurar jama'a ta duniya tayi kiyasin cewar a ko wace shekara, irin wadnanan yan baranda sukan karbi kudi misalin dollar miliyan 40 daga hannun masu son shiga Afirka ta kudu domin neman abin duniya, inda a karshe kwalliya bata biyan kudin sabulu.

Sudanese President Omar al-Bashir attends the opening of the second Arab-African summit in the coastal town of Sirte, Libya, 10 October 2010. According to media reports, the summit will hone in on key issues surrounding Palestinian-Israeli negotiations and the upcoming South Sudan referendum scheduled for January 2011, which could decide the future of a unified Sudan. This year's summit, organised by both the African Union and the Arab League, is the first for over 30 years. EPA/SABRI ELMEHEDWI +++(c) dpa - Bildfunk+++ usage Germany only, Verwendung nur in Deutschland
Omar al-BashirHoto: picture-alliance/dpa

Jaridar Süddeutsche Zeitung ita kuwa ta duba juyin juya hali ne a Masar da yadda hakan yake neman zama abin misali a kasar Sudan. A sharhinta, jaridar tace zanga-zanga da neman juyin juya hali yanzu dai sun cimma gwamnatin kama karya ta kasar Sudan. Ya zuwa yanzu, shugaba Omar al-Bashir ya sami nasarar hana wannan zanga-zanga ta wuce gona da iri, ta hanyar amfani da matakai masu tsanani na rashin imani, to amma jaridar Süddeutsche Zeitung tayi tambayar, shin ko zuwa wane lokaci ne shugaban na Sudan zai ci gaba da samun nasarar hana juyin juya halin ya wuce da mulkin sa.

Zaman lafiya da kwanciyar hankali har yanzu sun kasa samuwa a kasar Uganda da kasashe dake makwabtaka da ita. Jaridar Neues Deutschland tace tashin nakiyoyi da aka binne a karkashin kasa yanzu shine babbar matsalar dake addabar mazauna Uganda wadanda ke kusa da iyaka da Jamhuiriyar Democradiyar Kongo. Yayin da sojojin gwamnati a iyakar suke ci gaba da gwagwarmaya tsakanin su da yan tawaye, manoma dake kusa suna tserewa daga kauyuka da gonakin su. Abin dake biyo baya shine yan gudun hijira, yunwa da talauci da muzgunawa mata da yara a iyakar ta Uganda da Kongo.

Foto 1: agrar hütte kinder, Beschreibung: Bäuerin mit Kindern vor ihrer Hütte bei Lira im nördlichen Uganda. Aufnahme: Helle Jeppesen für DW, Aufnahmeort: Nördliche Uganda, Aufnahmedatum: Mai 2009, Bildtext: Jahrzehntelang würde ländliche Entwicklung kaum gefördert. Heute trifft extreme Armut global gesehen vor allem Frauen auf dem Land
Hoto: DW

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal