1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Goodluck Ebele Jonathan na shirin mulkin Nigeria na ƙarin shekaru huɗu

April 17, 2011

Jam'iyyar PDP mai mulki a Nigeriya ce ke da rinjaye a yawan ƙuri'un da aka kaɗa a zaben shugaban ƙasa da ya gudana ranar Asabar a Nigeria.

https://p.dw.com/p/10vBE
Hoto: DW

A Najeriya yayinda ake cigaba da kidayar kuri'un zaɓen shugaban ƙasar da aka kaɗa a ranar Asabar, a bisa ga dukkan alamu Jam'iyyar PDP mai mulki na shirin sake cigaba da jan ragamar mulkin ƙasar har na wasu shekaru huɗu masu zuwa.

A Kaduna kuwa duk da cewa an kammala zaɓen lami lafiya. A yanzu haka akwai tarin matsaloli da kuma rashin kwanciyar hankali da jama'a ke fuskanta.

A yayinda Jihar Jigawa sakamakon zaɓen da aka baiyana ya nuna Jam'iyar CPC ita ce ta lashe zaɓen a ƙananan hukumomi 23 daga cikin ƙananan hukumomi 27 na Jihar. Kamar yadda zaku ji a rahotanni da wakilanmu Ubale Musa daga Abuja, Ibrahim Yakubu dakada Kaduna da kuma Zainab Rabo Ringin daga jigawa suka haɗa mana.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala

Edita      : Zainab Mohammed Abubakar