1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Goita ya gana da tsoffin 'yan tawaye

Zainab Mohammed Abubakar
June 3, 2021

Jagoran gwamnatin riko a Mali Kanar Assimi Goita, ya gana da tsoffin 'yan tawayen Abzinawa, a daidai lokacin da kasar ke cikin hali na rashin sanin makomarta a siyasance.

https://p.dw.com/p/3uORa
Symbolbild - Tuareg in Mali
Hoto: picture-alliance/AP Photo//Rebecca Blackwell

A makon da ya gabata ne dai Kanar Goita ya kifar da gwamnatin rikon Malin, wadda aka kafa bayan kifar da gwamanatin zababben shugaba Ibrahim Bubacar Keita a watan Augustan bara.

Jagoran gwamnatin na yanzu dai, shi ne ya jagoranci kananan jami'an soji da suka kifar da Keita, biyo bayan zanga zanga bisa zargin cin hanci da rashawa a bangaren jami'an gwamnati, da gaza kawo karshen munanan hare haren mayakan jihadi.