1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fursunoni hudu sun mutu a Tehran

Abdul-raheem Hassan
October 16, 2022

Fursunonin hudu da suka mutu a gobarar suna jiran hukunci bayan an same su da laifin fashi da makami kuma suna zaman kurkuku a gidan yarin Evin.

https://p.dw.com/p/4IFiF
Gobara a gidan yarin Evin a Iran
Hoto: UGC

Hukumomin gidan yarin Evin ba su bayar da cikakkun bayanai kan dalilin tashin gobarar da kuma rikicin da ya barke tsakanin fursunonin ba.

Sai shedu sun ce a ranar Asabar an jiyo fashe-fashe da dama a cikin gidan yarin, bayan da gobarar ta tashi abin da jami'an kula da gidan yarin suka bayyana da rikici na cikin gida.

An shafe makonni ana zanga-zanga a Iran tun bayan sanar da mutuwar Masha Amini mai shekaru 22 a ranar 16 ga watan Satumba, kwanaki uku bayan da jami'an 'yan sanda suka kama ta a Tehran bisa zargin keta ka'idojin shigar mata a kasar.