1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobara ta halaka mutane a Aljeriya

Mohamed Tidjani Hassane Zahradeen Umar
July 24, 2023

Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan mutanen da gobarar daji ta yi ajalinsu a tsakanin daren Lahadi wayewar garin wannan Litinin.

https://p.dw.com/p/4UKIy
Gobarar daji da ta barke na ci gaba da barna a yankin Bejaia na kasar Aljeriya
Gobarar daji da ta barke na ci gaba da barna a yankin Bejaia na kasar AljeriyaHoto: Ammouri Abderahmane/REUTERS

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin cikin gidan Aljeriyar ta fidda, ta ce an samu akalla tashin gobara sau 97 a gundumomi 16, ko da yake sanarwar ta ce wutar ta fi yin ta'adi ne a Béjaïa da Bouira da kuma Jijel inda ta ritsa da rayukan jama'a.

Ma'aikatar ta kuma ce an yi nasarar canja wa iyalai 1.500 matsugunai yayin da iska mai karfi ke rura karfin wutar. Kazalika a yankin Tabarka ma da ke kan iyakar kasar da Tunisiya, an sanar da tashin gobarar a wannan Litinin, inda ta lakume filayen noma masu yawa baya ga gidajen al'umma.

Masu aiko da rohotanni sun ce jami'an kwana-kwana sama da dubu 10 sun bazama a halin yanzu domin shawo kan wutar da aka shiga kwana na biyu da tashinta, sai dai ana korafin ba su da isassun kaya aiki, sakamakon makalewar odar jiragen kashe gobara da kasar ta yi daga Rasha.

Tuni dai shugaban kasar Abdelmadjid Tebboune ya mika sakon ta'aziyya ga iyalen wadanda lamarin ya ritsa da su galibinsu fararen hula da kuma sojoji.