1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 30 da girka dimukaradiyya a Nijar

Salissou Boukari AH
July 29, 2021

A Jamhuriyar Nijar ana tunawa zagayowar cikon shekaru 30 da gudanar da muhawarar kasa da ake kira Conference Nationale wadda ta gudana a ranar 29 ga watan Yuli na 1990 wacce ta yi dalili samar da dimukaradiyya a kasar.

https://p.dw.com/p/3yG4s
Gebäude der Nationalversammlung in Niamey Niger
Hoto: DW

A duk bayan shekara goma ne dai shika-shikan da suka taka rawar gani a wancan lokaci na muhawarar kasa ne dai ke gudanar da bikin zagayowar ranar tare da tunatar wa al’umma muhimman batutuwa da wannan zama na tsawon watanni uku ya dauka da sunan kasar ta Nijar. Alhaji Sanoussi Tambari Jackou, wanda a lokacin muhawarar kasar yana dan shekaru 51, ya tunatar da muhimman ci gaban da muhawarar kasar ta kawo ma 'yan Nijar.

Tsokaci a kan rashin ba da muhimmanci na wasu 'yan siyasar ga ranar ta samar da da dimukaradiyya a Nijar

Sitzung des Parlaments in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Daga bisani Sanoussi Tambari jackou ya nuna fushinsa kan yadda ya lura cewa duk irin damar da wannan muhawara ta kasa ta bayar na samar da dimukuradiyya a kasar ta Nijar har wasu daga cikin 'yan kasa suka yi takara a mataki dabam-dabam, amma wannan bai ba su damar halartar wurin bikin tunawa da wannan muhimmiyar rana ba. Sai dai da yake magana Alhaji Nouhou Arzika wanda a wancan lokaci ya halarci muhawarar kasar cikin kungiyarsu ta dalibai ya ce duk matsalolin da ake ciki yanzu na rashin gudanar da kyaukyawan mulki muhawarar kasa ta tanadi yadda ta kamata a samu mafita. An dai gayyato tsofin shika -shikan na lokacin wannan muhawara ta kasa irin su sanoussi Tambari Jackou, Rabiou Daouda, Amman Moussa, Kaka Doka, Nouhou Arzika, Zakariya Abdourahaman Moustapha Kadi Oumani da dai sauransu inda ake bayar da tarihi dabam-dabam a gaban dalibai da sune ma suka fi yawa a zauran tunawa da zagayowar cikon shekaru 30 da soma muhawarar ta kasa a Nijar.