1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka za ta gudanar da sabon zaɓen 'yan majalisun dokoki

May 16, 2012

Sakamakon rarabuwar kawunan da ke tsakanin yan siyasar, Girka ta shiga halin tsaka mai wuya

https://p.dw.com/p/14wTY
Hoto: AP

Yanzu haka ana shirin gudanar da wani sabon zaɓen 'yan majalisun dokoki nan gaba a ranar 17 ga watan Yuni ,hakan kuwa ya biyo bayan gaza cimma nasara da aka yi tsakanin jam'iyyun siysar wajan kafa gwamnatin haɗaka a ƙarshen zaɓen da aka gudanar a ranar shidda ga watan Mayo.

Babban abinda ke zaman musababi na rashin zutuwar da ake fama da shi tsakanin yan siyasar shi ne tsatsauran ƙaidodoji na tsuke bakin aljihu da ƙungiyar ƙasahen Tarrayar Turai tare da sauran manyan hukumomi na lamuni na duniya suka giciyawa ƙasar gabannin samun tallafi na kuɗi biliyan dubu 130 domin kaucewa fadawa cikin matsalar tattalin arziki.Jam'iyar masu tsatsaura ra'ayi dai ta Syriza na neman a sake kwaskware yarjejeniyar ta ƙungiyar Tarrayar Turai amma kuma jam'iyar yan gurguzu ta Pasok ta yi karan tsaye a kai Evangelos Venizelos jagoran jam'iyar masu ra'ayin yan' gurguzu Pasok ya baiyana cewar tilas ne a samu mafita ''ya ce zamu je wani sabon zaɓe cikin wani hali mara sa tabas saboda son kai da fifiko da wasu suke nunawa akan su a maimakon ga ƙasa bakiɗaya.

ƙasar Girka na cikin halin tsaka mai wuya

Bilder vom derzeitigen Treffen von Präsident Papoulias mit den griechischen Parteichefs. From left to right, leader of the Democratic Left party Fotis Kouvelis, head of the Socialist PASOK party Evangelos Venizelos, leader of Conservatives New Democracy party Antonis Samaras, Greek President Karolos Papoulias, leader of the Coalition of the Radical Left party Alexis Tsipras and leader of the 'Independent Greeks', Panos Kammenos pose during a Political party leaders meeting at the Presidential Palace in Athens, on Tuesday, May 15, 2012. Greec's president met the leaders of five political parties, broadening talks to try and form a coalition government and end a nine-day deadlock in the crisis-hit country. (Foto:Aris Messinis, pool/AP/dapd)
Karolos Papoulias, tare da sauran yan siyasar ƙasar GirkaHoto: dapd

Shaka babu wannan hali da aka shiga a ƙasar da ke daf da talauce wa saboda basusukan da suka yi mata katutu na iya zama wani babban koma baya na kasa samun tallafin ƙasahen duniyar inda har jam'iyyun siyasar masu ƙyamar shirin tsuke bakin aljihun suka samu rinjaye a majalisar dokokin.Manolis Kottakis wani ɗan siyasar ne mai ra'ayin yan mazan jiya da ke yin sharhi akan al'amuran ƙasar ta Girka''ya ce abin tambaya a nan shi ne cewa KO wanan zai kasance hukumci ga wasu jam'iyyun siyasar akan ra'ayin da suke da shi na shirin tattalin arziki ya ce a yanzu ya kamata dukannin jam'iyyun siyasar su bada haɗin kai i wajan samar da masalha ga halin da ƙasar ta ke ciki.Nan gaba ne da aka shirya shugaba Karolos Papoulias zai baiyana gwamnati riƙon ƙawrya wacce za ta jagorancin gwamnatin kafin zaɓen da za a gudanar, kuma shugaban ya na cikin tattaunawa da ƙwarraru da manyan yan boko na ƙasar domin kauce wa abinda ka iya zama tarihi ga ƙasar wacce ake yiwa kallon cewa inda har ba ta yi nasara magance matsalar ba to kam ya na iya zamasanadiyar ficcewarta daga ƙungiyar Tarrayar Turai .

epa03213352 Greek Socialist PASOK party leader Evangelos Venizelos addresses journalists outside the Presidential Palace in Athens, Greece, 10 May 2012, after a meeting with President Karolos Papoulias. Greece's attempts to form a governing coalition entered a third and final round on 09 May, with PASOK leader Evangelos Venizelos becoming the latest politician to attempt to break the deadlock after elections produced no clear winner. Venizelos received a three-day mandate from the president to seek coalition partners following failed attempts by candidates from the two parties that gained the most votes in Sunday's election - the conservative New Democracy and the Coalition of the Radical Left, or SYRIZA. EPA/ALKIS KONSTANTINIDIS +++(c) dpa - Bildfunk+++
Evangelos Venizelos jagoran jam'iyar masu ra'ayin gurguzuHoto: picture-alliance/dpa

Ƙasashen ƙungiyar Tarrayar Turai na da fargaba akan makomar Girka

To sai dai minitan kuɗi na ƙasar Jamus ya ce a kwai buƙatar tsayarwar ƙasar ta Girka cikin ƙungiyar Tarrayar turai kuma ita ma shugabar asusun ba da lamuni na duniya Christine lagarde ta yi baiyani kamar haka:''ta ce idan har suka kasa bin kaidojin da aka giciya masu to a kwai hanyoyin da za a bi sai dai ta ce zasu kasance masu wahala.Kuma ko mai ta ke zama nan gaba a cikin watan Yuni za a san abinda al'ummar Girka za ta zaɓa.

Daga ƙasa za a iya sauraran sautin wannan rahoto

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umar Aliyu