1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka na shirin samun tallafi

February 20, 2012

Ministan kudi na ƙasar Faransa Francois Baroin ya ce duk abubuwan da ake buƙata sun kammala,

https://p.dw.com/p/145yW
ILLUSTRATION - Eine 2-Euro Münze, aufgenommen am Freitag (21.05.2010) in Düsseldorf. Griechenland reißt die mit EU, IWF und EZB für dieses Jahr vereinbarte Schuldengrenze. Grund ist die schrumpfende Wirtschaft. Um weiter zu sparen, sollen Zehntausende Staatsbedienstete gehen. Foto: Julian Stratenschulte dpa/lnw +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Domin ministoicin kulɗi na ƙungiyar ƙasashen da ke amfani da takardar kuɗin Euro ,su amince da bayar da tallafin kuɗaɗe a kaso na biyu ga ƙasar Girka da ke fama da matsalar tattalin arziki ,ministan ya ce ba za a ci gaba da jiraba a kan wasu hujoji guda biyu.''ya ce na farko majalisar dokokin Girka ta yi taro a makon jiya sannan gwammnatin ƙawancce ta yi alƙawari a rubuce cewa zata ƙaddanmar da sauye sauye.

Ministan ya tabbbatar da cewar shaka babu za a kai ga cimma yarjejeniya a taron da a ke yi a birnin Brussels sannan kuma ya ce ana buƙatar samin yardda bakanun da manyan kamfaoni na kuɗi masu ba da bashi da su kawo tasu gudun mowa domin yafe wani ɓangaren basusuka na ƙasar.Ana sa ran dai a ƙarshen taron ministocin na kuɗi zasu ba da izini na bayar da ƙarin tallafi na kudi biliyan dubu 130 ga ƙasar ta Girka.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Awal Balarabe