1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane fiye da 15,000 sun mutu a girgizar kasa

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
February 9, 2023

A kasashen Turkiyya da Siriya, ana ci gaba da ceton mutanen da bala'in girgizar kasa ya rutsa da su daga baraguzan gine-gine, a daidai lokacin da adadin mamata ya haura dubu 15

https://p.dw.com/p/4NGiG
Türkei Iskenderun Erdbeben Krankenhauseinsturz Bergungsarbeiten
Hoto: Umit Bektas/REUTERS

Adadin wadanda suka rasu sakamakon iftila'in girgizar kasar a Turkiyya da Siriya sun haura dubu 15 a wannan safiya, a daidai lokacin da aka shiga kwana na uku na aikin ceto ragowar wadanda suke da sauran numfashi a baraguzan gine-gine.

A wata ziyarar da ya kai a yankin da girgizar kasar ta daidaita, Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya ce duk da yake gwamnatinsa ta nuna sakaci, to amm ba wata hanyar da za a iya kaucewa wannan mummunan bala'i.

Jami'an 'yan sanda sun kama wasu gwamman mutane da suka zarga da wallafa bayanai a shafukan sada zumunta na zamani, suna masu caccakar gwamnatin Erdogan kan yadda ta nuna gazawa wajen kai daukin da ya dace  bayan afkuwar iftila'in.

Ita dai gwamnatin Ankara na shan suka daga bangarorin masu adawa ta hanyar shafukan sada zumunta kan rashin kokarin kai dauki cikin gaggawa.