Girgizar kasa ta kashe mutane a China
August 8, 2017Talla
A kasar China, akalla mutane 5 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon girgizar kasa da ta auku a wannan Talatar a yankin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar. Girgizar kasar mai karfin maki 6.5 a ma'aunin richter ta kuma raunata wasu mutane fiye da 63. Jami'an agajin gaggawa suna ci gaba da aikin ceto mutane daga baraguzan gine gine.
Rahotanni a kasar na cewa akwai mutanen da ke zaune a birnin Beijing mai tazarar kilomita dubu daya da dari biyu daga yankin da al'amarin ya auku da suka ce sun ji karar girgizar kasar. Al'amarin ya auku ne kusa da inda a baya aka taba samun girgizar kasa mai karfin maki 8 a shekarar 2008 inda aka rasa rayukan mutane fiye da 80,000.