1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girgizar kasa ta hallaka mutane 118 a China

Abdullahi Tanko Bala
December 19, 2023

Akalla mutane 118 suka rasu sakamakon girgizar kasa a yankin tsaunuka a arewa maso yammacin China.

https://p.dw.com/p/4aKLC
China | Rettungsarbeiten nach Erdbeben in Gansu Provinz
Hoto: Wang Xi/AP Photo/picture alliance

Girgizar kasar ta auku ne a tsakar dare da tsananin sanyi a yankin tsaunuka a arewa maso yammacin China.

Ma'aikin cetoaikatan agaji na ci gaba da aikin ceto a gundumar Gansu da Qinghai masu makwabtaka.

Girgizar kasar ta jikkata mutane fiye da 500 tare da lalata gidaje da tituna da turakun lantarki da na sadarwa.

Girgizar kasar mai karfin maki 6.2 ta auku ne kimanin karfe 12 na daren jiya litinin a cewar cibiyar nazarin girgizar kasa ta yankin.