1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shara ta mamaye garin Konakry

March 21, 2019

Bakin tekun babban birnin na Gini Konakry na cike da shara wanda har sharar na kokarin fin yashin da ke gabar tekun, haka kuma lamarin yake a cikin gari

https://p.dw.com/p/3FS3Z
Guinea Conykry Küste Stadt Kaloum
Hoto: DW/D.Köpp

Birnin na da akalla mutane miliyan biyu kuma wajen zubda shara daya tal gare su a bayan gari hakan yasa shara ke yawo a ko ina. kungiyoyi masu zaman kansu sun yi hobbasa don ganin sun kawo gyara a wannan bangaren.

Fatoumata Cherif na daya daga cikin masu fafatukar ganin an kawo karshen sharar da ke neman mamaye musu gari, inda ta ke daukar hotuna da ma bidiyon yadda garin nasu ke cika da shara tana watsa su a shafinta na facebook da twitter a kokarinta na janyo hankalin jama'a da ta yi ma taken "Rubbish selfies"

"An kaddamar da wannan gangami ne a shekarar 2016 don tattauna batun shara a babban birnin na mu wanda ke na 19 a jerin kasashe 25 da suka fi dati a duniya. wannan abin mamaki ne don lokacin da nake tasowa kasata ana mata taken "lu'u- lu'un Afirka. Da haka muna kokarin wayarwa da mutane kai dama janyo hankalin hukumomi don taka wa matsalar biriki."

Duk da kokari da jerin matakai da ake dauka a yan shekarun nan, har wayau ana cin karo da tulin shara a kan titunan Conakry babban birnin kasa, harta a kusa da manyan ma'aikatun gwamnati da ma ofisoshin jakadancin kasashen waje da ke a birnin.