1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Gbagbo zai iya komawa gida - Ouattara

April 7, 2021

Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara ya ce yana maraba da komawar tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo gida, bayan wanke shi daga laifukan cin zarafi. 

https://p.dw.com/p/3rhDk
Niederlande Den Haag I Prozess Elfenbeinküste am Internationalen Gerichtshof
Hoto: Jerry Lampen/AP/picture alliance

Shugaba Ouattara ya ce Gbagbo da na hannun damansa Charles Ble Goude na da damar komawa kasar ta Ivory Coast a duk lokacin da suka shirya. Furucin shugaban na zuwa ne mako guda bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC ta wanke su daga mumunar rikicin bayan zabe da ya jefa kasar da ke yammacin Afirka cikin wani hali a shekarar 2010 zuwa 2011.

Fiye da mutane dubu 3 ne suka rasa rayukansu a wani rikicin bayan zabe a shekarar 2010 a lokacin da Gbagbo ya ki sauka daga kan karagar mulki duk da shan kaye da ya yi a zaben kasar.