1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gaza: Ana ci gaba da kiran tsagaita wuta

Abdullahi Tanko Bala
December 19, 2023

Amurka ta ci alwashin ci gaba da bai wa Israila makamai a yakin da ta ke yi da Hamas yayin da a waje guda ta bukaci kai wa Falasdinawa karin taimakon jinkai a Gaza da yaki ya daidaita.

https://p.dw.com/p/4aKLD
USA, New York | Tagung des UN-Sicherheitsrats
Hoto: Charly Triballeau/AFP/Getty Images

Yakin wanda ya shiga wata na uku shi ne mafi muni a Gaza, inda ma'aikatar lafiya a yankin ta sanar da mutuwar mutane 110 a hare haren da aka kai sansanin yan gudun hijira na Jabalia da ke kusa da birnin Gaza.

Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin wanda ya kai ziyara Israila ya ce wajibi ne a samar da taimakon jinkai ga mutane kusan miliyan biyu da suka tagaiyara a yankin na Gaza.

Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya na shirin kada kuri'a domin sake kiran tsagaita wuta bayan da Amurka babbar aminiyar Israila ta hau kujerar na ki kan makamancin kudirin a baya.

Kwamitin sulhun Majalisr Dinkin Duniya ya dage kada kuri'ar zuwa wannan talatar domin ba da damar ci gaba da tattaunawa kan daftarin a cewar majiyoyin jami'an diflomasiyya.

Sakataren harkokin wajen Burtaniya David Cameron zai gana da shugabannin Faransa da Italiya domin neman tsagaita wuta mai dorewa.