Gaskiyar Magana: A Najeriya dokar hana batanci a shafukan sada zumunta da aka samar a shekarar 2015 ta yi silar zuwan wasu mutane gidan yari, shin me wannan dokar ta kunsa kuma ya masu mu'amalar shafukan sada zumunta ke kallon ta? Shirin na wannan makon ya tattauna da Abba Hikima masanin shari'a a Najeriya da kuma Fadila H Aliyu mai amfani da shafukan sada zumunta.