An gudanar da gagarimar sukuwar dawaki wacce ta hada dawakai a Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar wacce ta samu mahalarta daga jahohi 8 na kasar da kuma wasu mahalartan daga Tarayyar Najeriya. Babban tukwici a sukuwar dai shi ne tsabar kudi miliyan 3 na CFA ga dokin da ya yi nasara.