1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Garambawul a gwamnatin Masar

May 7, 2013

Shugaban Masar Muhammad Mursi, yayi wa majalisar ministocinsa garambawul da bai shafi fraim ministansa Hisham Qindeel ba.

https://p.dw.com/p/18Taf
Hoto: Imago

Watanni goma bayan rantsar dashi a matsayin shugaban kasa, shugaba Muhmmad Mursi na Masar, dake fuskantar gagarimar adawa daga jam'iyun yan hamayya da kungiyoyin masu fafutuka a kasar kan gazawa da suke cewa yayi wajen cimma alkawuran da yaiwa yan kasar a kokarinsa na nage kaifin adawar da ake masa, shugaban yai takaitaccen garambawul ga majalisar wanda ya shafi ministoci tara, ba tare daya shafi fraiministansa da ministocin cikin gida da watsa labarai

da yan adawa suka kafa musu kahon zuka ba, garambawul din da yan hamayyar suka ce, har yanzu ba'a rabu da Bukar ba.

"Maganin matsalar da muke ciki , ba kwaskwarima a hukuma da ta kasa kasau bane,kamata yai a kafa sabuwar gwamnatin ceton kasa wacca zata dinke barakar da aka samu tsakanin yan kasa,wacce kuma bata da wata aalaka da jam,iyun siyasa,domin yin haka ne kadai zai bada damar gudanar da sahihin zaben da zamu iya shiga."

A yayin da yan siyasa ke ci gaba da korafi kan wannan kwaskwarimar da akaiwa hukuma, su kuwa alkalai,da suka sanya kafar wando daya da fadar shugaban kasa a baya-baya nan, jefawa sukai suka cafke, bayan da aka nada, Ahmad Muhammad Sulaiman a matsayin ministan shari'a, wanda yai fice wajen kalubantar bangaren zartarwa, kan katsalandam din da takewa bangaren shari'a.

Kamar yadda garambawul din ya hada da ministan albarkatun man fetir da na kudi da tsare tsareda noma da sanya hannun jari, gami da ministan kayayyakin tarihi.

Kasancewar biyu daga cikin sabin ministocin,yan jam'iyar yan uwa musulmi ce ta shugaban kasa,da kuma rashin kawar da ministocin rarraba kayayyakin masarufi da matasa,wadanda suma din yan jam,iyar ta shugaban kasa ce, ya sanya masharhanta na hasashen yiwuwar sake kaiwa ruwa rana tsakanin yan hamayyar kasa da shugaban kasar. Wasu yan kasar da ake aron bakinsu a ci musu albasa dashi, sun bayyana irin fatan da suke da ita ga sabuwar hukumar.

Ägypten Kairo Proteste
Zanga-zangar yan adawa a MasarHoto: Getty Images

"Ina fata wannan hukumar zata samar da ayyukanyi ga masu zaman kashe wando,wadanda basu da matsuguni su samu,ina so in daina ganin yara kanana kan tituna suna watangaririyar neman aikin karfi,maimakon su kasance a makaranta."

Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Umaru Aliyu