1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin bukatar sanar da wanda ya ci zaɓe a Masar

Zainab MohammedJune 23, 2012

Dubun dubatan mutane sun yi dandazo a dandalin Tahrir, dake Alkahira da kuma dandalin Alka'id Ibrahim, kan abin da suka kira; A mayar da iko ga waɗanda shari'a ta bawa" .

https://p.dw.com/p/15K5h
Protesters demonstrate at Tahrir Square in Cairo June 22, 2012. Thousands of protesters filled Cairo's Tahrir Square overnight as Egypt's rival presidential candidates, Mohamed Morsy, an Islamist, and former general Ahmed Shafik accused each of trying to steal an election whose result is still not known five days after polling ended. REUTERS/Asmaa Waguih (EGYPT - Tags: CIVIL UNREST POLITICS ELECTIONS)
Hoto: REUTERS

Dubun dubatan 'yan Masar da ke goyon bayan ɗan takaran ƙungiyar 'yan uwa musulmi a zaɓen shugaban ƙasa, sun gudanar da zanga-zangar lumana a dandalin Tahrir dake birnin Alƙahira. Suna neman gwamnatin mulkin sojan ƙasar ta Masar ta janye dokar da ta kafa wacce ke bai wa sojoji damar ci gaba da fada a ji a harkokin mulki. Haka zalika magoyan baya Morsi suna neman hukumomi sun sanar da sunan dana takaransu a matsayin wanda ya lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasa. Ita dai hukumar zabe ta jinkirta sanar da sakamakon domin sauraran korafe korafen magudi da 'yan takaran biyu suka shigar gabanta. Kowanne daga cikin 'yan takaran wato Mohamed Mursi na kungiyar 'yan Uwa musulmi da kuma Ahmad Shafiq tsohon firaminista na  iƙirarin  lashe zaɓen. sai dai magoyan bayan Morsi na zargin  sojojin dake riƙe da mulki a  Masar da shirya maguɗi domin ayyana Shafiq a matsayin wanda ya yi nasara.

Shugaban hukumar zaben Masar Farouk Sultan ya karyata rahotannin cewa hukumarsa za ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da ake takaddama a ranar Asabar .Shugaban hukumar ya fada wa gidan talabijin na kasa cewa har yanzu hukumar  tana kokarin gudanar da bincike kan kurakuran da abokan hammayar biyu suka yi zargin an tafka.Haka nan kuma hukumar ta ce za'a bayyana wannan sakamakon ranar Lahadi amma kuma za'a ci gaba da wannan bincike har sai an tantance duk wasu bayanai an kuma yanke hukunci.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita      : Zainab Mohammed Abubakar