Gangamin adawa a dandalin Tahrir na Masar
June 5, 2012Zanga-zangar ta dandalin Tahrir dai, na zuwa ne adaidai lokacin da al'umar kasar ke cikin takaicin sakin wasu jami'an ma'aikatar kula da harkokin cikin gida, waɗanda ake shari'arsu tare da tsohon shugaban kasar, dangane da zargin kisan gillar masu juyin juya halin daya hambarar da gwamnatin mubarak. A ranar asabar ce dai Mubarak mai shekaru 84 da haihuwa, da tsohon ministan harkokin cikin gida Habib al-Adly, suka samu hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan wakafi, ayayinda aka saki wasu manyan jami'ai guda shida. Wannan hukunci dai ya samu mummunan martanin adawa daga al'ummar kasar, batu daya jagoranci bazuwar dubban mutane akan tituna tare da kira da ayi adalci. Al'ummar ta Masar dai sun bukaci da a yanke wa Mubarak hukuncin kisa tattare da mukarrabansa dake da hannu a kisan da akayi wa masu juyin juya hali.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman