1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

241111 Merkel Sarkozy Monti Treffen

November 24, 2011

A Alhamis ɗin nan ne shugabannin gwamnatocin Jamus da Faransa da Italiya suka tattauna a birnin Strassburg. Ganawar dake da nasaba da yunƙurin samar da mafita kan rikicin tattalin arziki daya dabaibaye ƙasashen Turai

https://p.dw.com/p/13Gak
Angela MerkelHoto: dapd

Taron na birnin Strassburg dake ƙasar Faransa dai wani yunƙuri ne  a ci gaba da ƙoƙarin da shugabannin ƙasashen da ke amfani da takardar kuɗi na Euro ke yi, na gano bakin zaren warware matsalar tattalin arziki sakamakon basussuka da suka yi wa wasu ƙasashen katutu.

Sarkozy da ke zama mai masaukin baƙi da shugabar gwamnatin Jamus Merkel dai su ne ke taka rawa a yunƙurin shawo kan rikicin tattalin arzikin, sai dai a wannan karon sun gayyato sabon priministan Italiya Mario Monti. Mai masaukin baƙin taron kuma shugaban Faransa Sarkozy ya yi tsokaci dangane da muhimmancin taron shugababbnin gwamnatocin ƙasashen uku masu mafi ƙarfin tattalin arziki a nahiyar turai.

Nicolas Sarkozy in Frankfurt 19. Oktober 2011
Nicolas SarkozyHoto: dapd

" Italiya ƙasa ce da ke da muhimmanci a jerin ƙasashe dake amfani da takardar kuɗi na Euro, kuma ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙasashe masu ci gaban masana'antu a Duniya".

Wannan ganawa ta Merkel da Sarkozy da kuma Monti domin tattauna rikicin tattalin arzikin nahiyar, na nuni da cewar suna goyon bayan sabuwar gwamnati Italiya. kazalika a nahiyar Turai bawai tarayyar Jamus a matsayin ta ƙasa mafi tattalin arzki  da abokiyarta  Faransa da ke ɗaya  ɓangare kawai ba, wata kila priministan Mario Monti na Italiya zai iya taka rawar shiga tsakanin ɓangarorin biyu a sabanin da ke tsakaninsu na warware rikicin tattalin arzikin ƙasashen dake amfani da kuɗin euro.

A wannan makon ne 'yan siyasan faransan suka koka dangane rashin samun nasarar Jamus wajen amfani da manyan bankuna, domin warware rikicin tattalin. Tuni dai shugabar gwamnatin Angela Merkel ta faɗawa majalisar dokoki ta bundestag cewar, gwamnati ba zata amince da sayen hannayen jari fiye da kima daga kasashen turai dake fama da karayar tattalin arziki ta karkashin manyan bakunan turai na Central ba.

Merkel ta jaddawa 'yan majalisar Jamus cewar, alhakin  Manyan Bankunan ne tabbatar da kare martaba da darajar kudi, kuma suna da 'yancin gashin kansu.

Mario Monti in Brüssel
Mario MontiHoto: dapd

" Wannan 'yan cin tafiyar da ayyuka ya shafi kowane bangare, koda suna wani abun kokuma basa komai. Domin hakan yake ga kotun tsarin mulkin kasa, kuma yana da matukar muhimmanci kasashen turai su yi nazari dangane abun da irin 'yancin wadannan hukumomi suka ta'allaka akai".

A taron na yau dai Faransa ta cigaba da matsin lamba wa Jamus  na sauya matsayinta na kin amince wa Babban Bankin Turai sayen hannayen jari babu iyaka daga kasashen dake fama da matsalar karayar tattalin arziki.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita          : Umaru Aliyu