1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bukaci a hukunta Jammeh na Gambiya

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 25, 2021

Wata hukuma da aka dorawa alhakin binciken mulkin shekaru 22 na tsohon shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh ta kammala binickenta na tsawon shekaru uku.

https://p.dw.com/p/43UfW
Gambia Ex Präsident Yahya Jammeh
Tsohon shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh da ke gudun hijiraHoto: picture-alliance/dpa/Taiwan Press Office

Hukumar Bincike da Sansantawa da Biyan Diyyar TRRC dai, ta bukaci a yanke wa Yahya Jammeh hukunci kan kisa da azabtarwa da sauran cin zarafi da ya aiwatar a lokacin gwamnatinsa. Hukumar da aka daurawa alhakin bincike da sasantawa da kuma biyan diyya, ta mika sakamakon binciken nata ga Shugaba Adama Barrow kwanaki tara gabanin zaben da tsohon shugaban kasar Jammeh da ke gudun hijira ya bukaci magoya bayansa su zabi gamayyar jam'iyyun adawa. Kimanin shaidu 400 ne dai, suka bayar da shaida a gaban hukumar ta TRRC da suka hadar da wadanda aka ci zarafinsu ko aka kashe 'yan uwansu da kuma wadanda suka aikata laifin. Shugaba Barrow ko kuma wanda zai gaje shi, na da tsawon watanni shida ya bayyana yadda zai aiwatar da rahoton da kawo yanzu ba a bayyana cikakken abin da ya kunsa ba.