1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gagarumar zanga-zanga a Masar bayan sallar Juma'a

January 28, 2011

Ma'aikatar cikin gidan ƙasar ta Masar ta yi gargadɗin ɗaukar matakan da suka dace akan masu yin bore sannan ta yi kashedi da su kiyayi yin zanga-zanga a yau.

https://p.dw.com/p/106Nb
Masu boren ƙin jinin gwamnati a Masar na ci-gaba da tada ƙayar bayaHoto: AP

Gwamnati a ƙasar Masar ta yi gargaɗin cewa za ta ɗauki tsauraran matakan tsaro ga masu neman sauyi a zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a yau bayan sallar juma'a domin ƙin jinin gwamnati. Gargaɗin kashedin wanda ofishin ministan cikin gida ya baiyana a cikin daren Alhamis zuwa yau Juma'a ya ce ba za su yi da wasa ga jama'ar da ke bazuwa akan tituna domin tada zaune tsaye ba.

A karon farko dai ƙungiyar 'yan'uwa Musulmi ta ce za ta shiga cikin zanga-zangar kuma yanzu haka tsofon shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya na duniya Mohammed Elbaradei wanda ya isa a birnin Alƙahira domin halartar boren, ya ce a shirye ya ke ya jagoranci gwamnatin wucin gadi da zaran gwamnatin ta Hosni Moubarak ta fadi sanan kuma ya ƙara da cewa.Bamu so ta kaimu ba ga bazuwa kan titunan mun yi ta kokarin bi hanyoyin lallama amma abin ya ci tura. Tun a ranar talata da ta gabata ne jamaa a kasar ta tunisiya ke gudanar da jerin zanga zanga da ta bazu ko'ina a cikin yankunan domin neman sauyi ga gwamnatin mulkin kama karya ta Hosni Moubarak wanda ke kan karagar mulki kusan shekaru 30.

Kawo yanzu dai mutane bakwai suka mutu yayin da ake tsare da wasu dubai, kuma har a yau 'yan sanda su kama ƙarin wasu mutane 20 na ƙungiyar 'yan'uwa Musulmi.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita: Mohammed Nasiru auwal