1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 55 na shugabancin gado a Gabon

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 9, 2023

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba ya sanar da aniyarsa ta neman wa'adi na uku, a matsayin shugaban kasar Afirkan da ke da arzikin albarkatun man fetur.

https://p.dw.com/p/4Tduj
Gabon | Siyasa | Takara | Shugaban Kasa | Ali Bongo Ondimba | Gado | Omar Bongo Ondimba
Shugaba Ali Bongo Ondimba na GabonHoto: STEEVE JORDAN/AFP

Mai shekaru 64 a duniya Shugaba Ali Bongo Ondimba ya bayyana hakan ne, a wani jawabi da ya yi ga dandazon magoya bayansa da aka watsa kai tsaye a shafinsa na Facebook. A shekara ta 2009 ne dai, Bongo ya karbi shugabancin Gabon a hannun babansa Omar Bongo Ondimba da ya kwashe shekaru 41 a kan karagar mulki. Hakan dai na nuni da cewa, iyalan na Bongo sun kwashe shekaru 55 kawo yanzu suna mulki a Gabon. Koda yake da kyar Shugaba Ali Bongo ya sha a zaben 2016, inda ya dara abokin hamayyarsa Jean Ping da ya bukaci a sake zaben da kuri'u dubu biyar da 500 kacal. Sai dai duk da yadda jam'iyyun adawa ke ganin iyalan Bongo sun mayar da mulkin Gabon gadon gidansu, sun gaza fitar da mutum guda da zai iya fafatawa da Ali Bongo ya wakilce su a zaben da ke tafe. A yanzu haka dai, akwai 'yan adawa 15 da suka bayyana aniyarsu ta yin takarar shugabancin kasar.