1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aubameyang ya bar taka leda a Gabon

Abdul-raheem Hassan
May 19, 2022

Fitaccen dan wasan kwallon kafar nan Pierre-Emerick Aubameyang ya yi ritaya daga takawa kasarsa ta haihuwa wato Gabon leda,kamar yadda Hukumar Kwallon Kafa ta kasar ta tabbatar.

https://p.dw.com/p/4Ba2r
Fußball I Pierre-Emerick Aubameyang I Gabun
Hoto: Carl de Souza/AFP/Getty Images

Aubameyang mai shekaru 32 a duniya, shi ne dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a Gabon da kwallaye 30 a wasanni 72 bayan shafe shekaru 13 yana murza leda a kasar.

Yanzu haka dai dan wasan Aubameyang na takawa Bercelona leda, bayan da Arsenal ta soke kwangtiraginsa a watan Janairun wannana shekara. A yanzu haka dai ya taimakawa sabuwar kungiyar tasa wato Bercelona samun gurbin shiga gasar zakarun Turai, inda ya zura kwallaye 11 a wasanni 16 na da ya buga a kaar ta La Liga a Spain.